Sanata Uba Sani ya ‘dauki nauyin karatun ‘ya ‘yansa harzuwa jami’a tare da kyaur milyan biyu 2m ga Iyalansa bayan ‘yan Bindiga sun harbe shi.

Sanata Uba sani mai wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya ya dauki nauyin karatun iyalan Hon Lirwanu Gadagau tare da Bawa iyalansa kyautar ku’di naira Milyan biyu 2m Sanatan ya bayyana hakan a Lokacin da yakai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin.

A Lokacin da yake jawabinsa Sanatan yana cewa ba zamu barku haka nan ba zamu daukin ‘ya ‘yansa Kamar yadda muka dauki namu zamu dauki nauyin karatun su harzuwa matakin jami’a zan Kuma bayarda naira Milyan biyu a bawa iyalan insha Allahu Kuma Allah Ya jikansa inji Sanatan.

Sanatan

ya bayyana kyakkyawar dabi’ar ‘dan majalisar yace mutun ne mai Amana Mai alkawari ya Kuma ce abin da ya auku dashi ya auku damu baki daya bama iya shi ba Abu ne dake faruwa da jama’a aduk kasar nan Kuma muna taimakon kamar yadda na Fadi Abu ne daya tayar Mana da hankali kuma dole ne wannan jami’ai su tashi a cigaba da neman wannan ‘yan ta’adda Kuma Kamar yadda ka sani mu a majalisar dattijai da ta wakilai duk wasu kudi da ake bukata an bawa jami’an tsaro Amma haryanzu wannan Abu yaki tsayawa don Haka zamu cigaba da kokari domin ganin an kawo tsaro a kasar nan da yardar Allah inji Sanata Uba sani.

A nasu bangaren ‘yan uwan marigayin da iyalansa sun mika godiya ga Sanata Uba sani bisa ta’aziyya da Kuma wannan yunkuri nasa na kula da iyalan dan majalisar.

Hon Lirwanu Gadagau ‘dan Majalisar Jiha ne dake wakiltar karamar hukumar Giwa ta yamma wanda idan Baku manta ba a ranar Larabar data gabata ne wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan bindiga ne Suka harbe shi a hanyar Kaduna zuwa Zaria Wanda hakan yayi sanadiyyar rasa ransa.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *