Sanata Uba Sani Ya Gina Cibiyar koyar da sana’o’i ga matasa ‘ya ‘yan talakawa a jihar kaduna.

Yadda Sanata Uba sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya ya gina katafariyar cibiyar koyar da sana’o’i a Sabon garin Nasarawa Tirkania dake karamar hukumar Chikun dake Jihar kaduna
Wanda yanzu Haka an dai mika aikin watanni biya 2 da Suka wuce Yanzu haka cibiyar na hannun Jagorancin karamar hukumar ta Chikum an Samar da cibiyar ne domin koyar da Mata da matasa sana’o’i kala domin dogara da Kai.

Idan

baku manta ba Sanata Uba sani shine Shugaban kwamitin inshora bankuna da Sauran harkokin kudi, Sanatan shine Jagoran wajen kaddamar Bayarda Rance ga Manoma daga CBN Wanda bankin NIRSAL ke bayar Wanda kawo manoma Yan Nageriya sun rabauta da tsarin.

Sanata Uba sani shine Sanata mafi aiki a majalisar ta Tara kamar yadda hukamar Bincike ta Midterm Dake majalisar ta tabbatar a satin daya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *