Sanata Uba Sani ya gina Makarantun ilimin fasahar Sadarwar zamani a mazabar sa.

A jihar kaduna A kokarin sa na Samar da ingantaccen ilimin zamani ga matasan ‘yan mazabarsa Sanata Uba Sani ya gina tare da samar da kayan aikin cibiyoyin Fasahar Sadarwar Zamani ICT a wasu kananan hukumomi cikin bakwai da Sanatan ke wakiltar a majalisar dattijan Nageriya

An Samar da cibiyoyin ne a Makarantun da Suka ha’da da…

  1. Maimuna Guarzo sakandirin gwamnatin dake Tudun Wada, a Kaduna ta Kudu,
  2. Makarantar sakandaren gwamnati, Kawo, Kaduna ta Arewa da kuma
  3. Makarantar sakandaren gwamnati, Turonku, karamar hukumar Igabi. (Ana Kan aiki)

Samar

da wannan makaratun zai ba wa malamai da ɗaliban Samun damar zama masu ilimin kwamfuta domin shiga jerin sahun sauran mutanen zamanin masu ilimin fasahar Zamani a duk matakan duniya.

A Cikin ko wacce Makaranta an Samar da na’urori masu kwakwalwa (Computer) har guda ‘dari biyar 500, Jimulla dubu da ‘dari biyar 1,500.

Ana sa ran Sanatan zai Samar da irin wannan makaratun a duk fa’din kananan hukumomin da yake wakilta a jihar kaduna.

Anfanin wannan cibiyoyi na
Fasahar Sadarwa (ICT) a cikin tsarin ilimi shine Samar da ilimi ta Hanyar amfani da fasahar sadarwa domin tallafawa da haɓaka hanyoyin isar da bayanai kala-kala a matakin Duniya.

Binciken duniya ya nuna cewa kafa Cibiyoyin ICT na iya haifar da ingantaccen tsarin ilmin ɗalibai da ingantattun hanyoyin koyarwa Cikin sauƙi, Rahoton da Cibiyar Ilimi ta Multimedia ta bayar a kasar Japan, ya tabbatar da cewa karuwar amfani da fasahar sadarwa ta ICT a cikin ilimi tare da hada fasahar da manhajar karatu yana da Matukar tasiri mai kyau da nagarta ga nasarorin dalibai musamman ɗaliban da ake ci gaba da Neman hanyoyin sanin ilmin fallasa su ta hanyar fasaha masu anfani da fasahar irin wannan cibiyoyi an kwatanta su Cewa basu da sa’a cikin tsarin fahimtar karatun Zamani.

Bincike ya tabbatar da cewa Rashin Ilimi na ‘daya daga cikin manya manyan Matsalolin dake saka matasa shiga harkokin ta’addanci, duba da Cewa jihar kaduna na ‘daya daga cikin Jihohin Arewa maso yamma dake fama da hare-haren ta’addancin ‘yan Bindiga, tabbas cigaba da Samar da ire-iren wannan cibiyoyi zai taimaka wajen dakile shigar matasa wannan harka ta ta’addanci.

Sanata Uba Sani na ‘daya daga Cikin Jerin ‘yan majalisar dattijan Nageriya dake kokarin ganin an raba matasa da Jahilci da Zaman Banza ta Hanyar Samar da sana’o’i domin dogaro da kawunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *