Sarauniyar Ingila Quen Elizabeth ta ki amincewa da karbar kyautar zama tsohuwar Shekara.

A wani Rahoto dake Zuwa Mana na Cewa Sarauniya Elizabeth ta II ta yi watsi da kyautar ‘Oldie of the Year’, tana mai cewa ba ta dace da ka’idojin kyautar ba.

Martanin mataimakinta sakataren ta mai zaman kansa, Tom Laing-Baker Yace sun karanta kyautar sosai saboda haka Sarauniyar ba ta yi imani sa Cikakkun ƙa’idodin da suka dace don samun damar karɓar kyautar ba da fatan za ku sami wanda ya fi Ni cancanta.

Jama’a da dama na kallon Cewa Sarauniyar tayi fatali da kyautar ne bisa nazarin Cewa ita batayin tsufan da zata iya karbar kyautar ba duba da Cewa kyautar girmamawa ce ta Tsofaffi tukuf-tukuf.

Credit:

Twitter | OldieMagazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *