SERAP ta bukaci Buhari da yayi gaggawar gano barayin da suka sace bilyan 3.1bn a Gwamnatin sa.

Kungiyar kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa, SERAP, ta yi kira ga gwamnatin tarayya, kan badakalar satar kudade da aka tafka a ma’aikatar kudi har Naira Biliyan 3.1m wanda ba a san ko su waye suka sace ba.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta bukaci shugaban kasa Buhari da ya yi amfani da kyawawan ofisoshin sa wajen umartar babban lauya na tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami, SAN, da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su binciki zargin bacewar sama da N3bn na dukiyar al’umma Wanda aka sarrafa ko kuma aka karkatar da su daga Ma’aikatar Kudi ta Tarayya.”

Kungiyar

ta ce an tattara wadannan zarge-zargen ne a cikin rahoton shekara ta 2018 da 2019 da babban mai binciken kudi na tarayya ya tantance.

SERAP ta ce: “Duk wanda ake zargi da hannu a cikin lamarin to ya fuskanci hukunci kamar yadda ya dace, idan akwai isassun shaidun da za a iya yarda da su, kuma duk wasu kudaden gwamnati da suka bata ya kamata a kwato su gaba daya.”

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 24 ga Disamba 2021, kuma mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, kungiyar ta ce, “Rahotanni sun nuna babban cin zarafin jama’a ne. A matsayinta na mai kula da kudaden jama’a, ya kamata ma’aikatar kudi ta tabbatar da bin ka’idoji da tsare-tsare na gaskiya da rikon amana.”

A cewar SERAP, “a matsayinta na babbar hukumar gwamnati, ma’aikatar tana da muhimmin aiki na tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin kashe dukiyar kasa. Wannan yana nufin samar da jagoranci mai karfi a kokarin da ake na dakile cin hanci da rashawa a sassan gwamnati.”

“Wannan jagoranci yana da mahimmanci ga ma’aikatar don jin daɗin amincewar jama’a

SERAP ta ce, “ Zargin da ake yi na bacewar N3,143,718,976.47 na kudaden jama’a, shi ma zai kasance a fili karara ya zama wani babban salo na karya dokokin yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kuma wajibcin yaki da cin hanci da rashawa na kasa da kasa da suka hada da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa da Najeriya ta kasance tana yi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *