Shari’ar Sheikh Abdujabbar Lauyoyin Gwamnatin Kano sun Karya doka a kotu~Aliyu samba.

A yau ne wata Kotun shari’ar Muslunci ta Alƙali Ibrahim Sarki Yola dake gidan sarki kofar kudu ta cigaba da sauraren ƙarar da gwamnatin jihar Kano ta shigar da Sheikh Dr Abdujabbar Kabara bisa tuhumar sa da suke ce suna yi masa.

A yadda shari’ar ta kasance a yau, gwamnati tayi abinda ya saba da dokar aikin lauyoyi na shigo da manyan lawyoyi cikin shari’ar wanda suka kai Matakin SAN, kuma bugu da ƙari suka nemi kotu da ta yi amfani da sabon cajin da suke son ƙaƙabawa saɓanin wanda suka shigar da kara wajen ƴan sanda a baya.

Barista

Bakaro Wanda shine jagoran lawyoyin Maulana ya bayyanawa kotu cewa dokar da aka dogara da ita da ta basu wannan izini bata cikin tsarin mulki Najeriya na 1999 da akayiwa gyara, ya kuma bayyana cewa Inda yace shashe na 211, karamin sashe (B) a cikin baka babu shi a cikin kundin tsarin mulkin kasa na 1999.

Sannan Barista Bakaro ya cigaba da cewa: “Wannan sabon chaji da suka kawo gaban wannan kotu, wanda suka hujja dashi, babu shi a cikin kudin tsarin mulki na kasa na 1999. Saboda haka dashi babban lauyan Gwamnatin Jihar Kano da su Manyan Lauyoyin masu mukamin SAN da aka baiwa izinin da ragowar Lauyoyin dukkan su basu kawowa kotu dokar data dace da wannan kotun da zata dogara da ita ta sahale musu hakan ba”

Barista Bakaro ya Kara da cewa yin hakan kaman mutum ne yace yayi kyauta da abun da babu shi, dan haka sabon cajin nan babu shi dan su ne suka saka hannu, babu hurumin yin hakan a dokan ce.

Suka ta biyu da Barista Bakaro ya yi shine fadinsa cewa: “Su lauyoyi SAN dokar bata basu damar bayyana a gaban kowace kotu ba wacce tayi kasa da babbar kotun jiha ba, bi ma’ana doka bata basu damar bayyana a irin wannan kotu data kasa da ita ba”

“kowane lauya ya sami ikon aikin lauya ne bisa dokar da zan karanto: sashe na biyu (Legal practitioners ACT) shine ya kirkiri wani kwamiti da lauyoyi zasu gabatar da aikin su na shari’a a gaban kowacce kotu. Shi kuma shashe na 5 karamin sashen na (7) shine ya bayar da dama kuma yayi doka ga lauyoyi masu mukamin SAN” inji Barista Bakaro

Ya cigaba da cewa: “sashe na 3 na dokar aikin lauya ya bayyana karara irin kotunan da lauyoyi masu mukamin SAN Zasu iya tsayawa a gaban ta, Sannan wata doka ta Sashe (4) ta aikin lauya ta haramtawa Lauya mai mukamin SAN damar da zai gabatar da kowa ce irin takarda ko wani sabon chaji ko shaida a gaban wata kotu da ba a basu dama ba kamar irin wannan kotu”

Barista Bakaro yace zasu baiwa kotu kwafi wadannan dokoki, kuma ya kara da cewa “Da wadannan dalilai ne suke sukar hurumin kotu kan bayar da sauraro ga lauyoyin dake kara da takardar chajin da suka kawo gaban kotu da suka sa hannun, wanda a dokance batacciya ce tunda sun shigar da wannan chaji ranar 13 ga watan Agusta 2021”

Gaba ta 3 da Lawya Barista Bakaro yayi suka shine fadinsa a kotu cewa:

“A kaddara suna ma da damar, ba dan sun yarda ba, a tsarin dokar shari’ar Musulunci ba’a chanja tuhuma ko zargi”

Barista Bakaro yace a “Yazo a littafin bahaja, a juzu’i na 1 shafi na 105 da littafin bayyara juzu’i na daya shafi na 36 da bayanin cewa: (da zarar mutum ya gabatar da da’awar sa a gaban kotu, mutum bashi da hurumi ko damar sake wani abu da ya gabatar tun da farko agaban alkali”

Barr Rabiu daya daga lawyoyin Maulana Yace: abin da nasoshi suke nunawa shine idan kotu tayi duba da asalin da’awar da aka gabatar mata tun a farko, ta ranar 16 ga watan 7 tare da wannan sabuwar da’awa da suke so su gabatar da ita a yanzu, kotu zata ga akwai kare-kare da rage rage da raurawa da sabani da dama daga ta asali. To dan haka wannan kotu bata da hurumin ta basu dama su shigo da wannan da’awa domin shari’ar musulunci bata basu wannan dama ba, wanna itace sukar su ta 3.”

Barista Sale Bakaro yace: “da wannan ne muke neman alkali da ya koma kan tuhume tuhumen farko da aka yiwa Sheikh Abduljabbar tare da korar wadannan daga cikin wannan shari’a dan yin adalci.

A wannan gaɓar ne aka baiwa Lauyoyin gwamnati damar su mayar da martani:

Barista Sa’id daga lawyoyin gwamnati Yace: kamata yayi lauyan wanda ake kara ya bari a karanto sabon chaji da ake yiwa wanda yake karewa sannan ya zayyano dukkan abin da ya fada, A bisa doka wajibi ne a karanto chaji, idan an gama shine sai ayi suka ko a goyi baya, in akayi duba da shashe na 390 karamin sashe na (2) na Kundin tsarin mulki kasa. Dan haka ya janye maganganun da yayi sai bayan an karanto chajin sannan sai yayi kowacce”

Sun kuma nemi kotu ta karanto cajin da aka kara sannan a cigaba da Shari’a, saidai Barista Bakaro yace:

“wannan sashe da Lauyoyin gwamanti ya gabatar na magana ne kan korafin da aka gabatar tun da farko, a ranar 16 ga watan Jiya na Yulin an kawo wanda ake zargi gaban kotu, aka karanta masa chaji ta hanyar rahoton yan sanda na (FIR), bai kuma amsa aikata laifin ba, dan haka ya riga ya amsa karar da akai a kotu, wanda hakan ke nuni da an fara shari’a.”

“Sannan sashe na 2 na dokar ACJN tayi bayanin menene chaji, wanda ita FIR din da aka gabatarwa da Kotu itama Chaji ce”

A ƙarshe mai Shari’a Alƙali Ibrahim Sarki Yola yace ya ɗage sauraron ƙarar saboda hujjojin da aka gabatar masa sunyi tsauri da bazai iya yanke hukunci nan take ba, saboda haka ya ɗage Shari’ar zuwa 2 ga watan Satumba, 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *