Sheik Pantami da Rahama sadau sune aka fi Suka da caccaka na 2021 a Shafukan ‘yan Arewacin Nageriya.

2021 Rahotanni da bincikenmu na MIKIYA kan fitattun Mutanen da suka Shahara a yankin Arewacin Nageriya wa’yanda ‘yan Nageriya suka fi Suka da caccaka a shafukan sada zumuntar zamani na Shekara ta 2021 Farfesa Sheikh Ali Isah Pantami da Jarumar Fina finan hausa Rahama Sadau sune sahun gaba-gaba a Jerin wa’yanda aka fi suka da caccaka.

Farfesa Sheikh Ali Isah Pantami Minisatan Sadarwar Nageriya yana shan Suka mai girman gaske daga ‘yan Nageriya Hakan baya rasa na Saba da yadda Shehun malamin yasha sukar Gwamnatin Tsohon Shugaban kasar Nageriya Dr Goodluck Ebele Jonathan Kan Lamarin tsaro a Lokacin Gwamnatin ta Jonathan, Malam Pantami ya Kasance Yana hawa mimbari Sallah tare wuraren wa’azin sa yana sukar Gwamnati Yana kuka Yana karanta al’kunut da nufin Allah ya Karya Jam’iyar PDP da mulkin ta musamman yadda ta Gaza wajen kawo karshen Matsalar ta’addanci a wan’can Lokacin, Haka zalika Malam Pantami yasha alwashin kauracewa daga shiga harkokin Gwamnati Dana Siyasa amatsayinsa na malamin Addinin Islama.

Farfesa

Ali Pantami yayi addu’a da Cewa Randa za’ayi zalunci a nageriya Kuma shi Bai fito Yace anyi zalunci ba to gwanda Allah ya dauki rayuwarsa kafin Lokacin, bisa Hasashen ‘yan Nageriya na cigaba da sukarsa ne Sakamakon yadda a yanzu malamin ya gaza yin ire-iren addu’o’in da yayi a Lokacin Gwamnatin Jonathan a Kan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari musamman a dai-dai wannan Lokaci da ake fama da Matsalar ta’addancin ‘yan Bindiga a arewacin Nageriya wanda yanzu Haka suke cigaba da Kashe Kashen Al’umma , Wasu na ganin Malam Pantami yayi shiru domin an bashi mukamin Minisatan a wannan Gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari Mai Mulki.

Rahama sadau na daya daga Cikin taurarin Jaruman masana’antar Kanywood ta fara Samun Suka da caccaka daga Jama’a ne tun bayan data fara wallafa wani Hoto dake nuni da zuwanta kasar India domin daukar wani fim tare da jaruman na kasar India, Jarumar Wacce ta juma dauke da burin Shiga Cikin Jaruman India domin fitowa a Fina finan su ta wallafa wani hoto tare da Fitaccen jarumi a masana’antar Fina finan kasar ta India wato Jarumi Vidyut jammwal A ranar goma 10 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2021 Lamarin da ya jawo Jama’a da dama suka caccaki Jarumar amatsayin wani lamari da suke kallo Bai dace ba Kasancewar al’adar Fina finan kasar India sun sha bam-bam dana hausa wanda Jarumar ta Saba fitowa, duk da Cewa Jarumar Tasha caccaka daga masu bibiyar a shafukan ta na sada zumuntar Zamani amma Hakan Bai hana ta wallafa wasu sabbin hotuna ba a Lokacin da ake tsaka da daukar fin din a kasar ta India.

A Lokacin ziyarar Jarumar ta ziyarci ofishin jakadancin Nageriya ta Kuma gana da jakadan Nageriya zuwa India wato Ambasado Ahmad Sule.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *