Sheikh Bello yabo Yace dasu akayi anfani wajen kamfen ga Buhari.

A wani gajeran Bidiyon sheikh Bello yabo dake yawo a kafafen sada zumintar zamani an jiyo malamin Yana sukar shugaban Muhammadu buhari Kan salon mulkinsa musamman yadda ya soke batun tallafin Ayyukan hajji, farkon maganar ta shehun malamin an jiyo shi yana Mai cewa tun farkon Gwamnatin buhari nasan za’a Sami matsala malamin yace kunsan dalilin? Yace mu fa aka ‘diba mukayi kamfen tun shekarun 2003-7-11 wasu kasa-kasai da nayi sune aka dunga kamfen dasu harzuwa 2015 muka dinga Kiran mutane muka ha’da su da addini duk inda wata AYAH take sai da muka jawo ta hakane ko ba haka bane? Inji malam Bello yabo.

Malamin

ya kara da cewa amma kusan abinda ya bamu mamaki? Addinin mukayi anfani dashi mukayiwa buhari kamfen Kuma indai baiji kaset din kowa ba nasan yaji nawa domin a Lokacin akwai mutumin da yake aikowa yace yaji labarin anyi Sabon kaset azo wajen malam a amso Masa sabo. Yaji kaset din ko bai jiya ba kuma masu karba suna nan idan ‘daya ya mutu daya Yana nan a raye.

Amma buhari bai hanamu ba Lokacin mukayi anfani da addini mukayi Masa kamfen Amma buhari ya na hawa da aka fito Masa da batun aikin hajji sai yace aiki haji ai aikin ibada ne sai yace it’s unconstitutional undemocratic unfair sune kalmomin da yayi amfani dasu Kan a ‘dibin ku’din Gwamnati ayi aikin addini dasu sai ya bude baki yace don haka yanzu tallafin da ake bayarwa ya cire buhari yace ya cire hannunsa a aikin Allah.

Buhari ya cire hannunsa a aikin Allah shiyasa shima Allah ya cire hannunsa aikin buhari Kuma Allah ya cire hannunsa a aikin buhari gayamun yadda za’ayi aikim buhari ba zai lalace ba? Shiyasa kuyi ta addu’a Amma ba zata anfani ba- Inii bello yabo…

2 thoughts on “Sheikh Bello yabo Yace dasu akayi anfani wajen kamfen ga Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *