Shugaba Buhari ya gargadi masu motocin dake cin zarafin hanyoyin Nageriya ta Hanyar lodin wuce ka’da.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika bin ka’idojin manyan tituna na kasar nan a kodayaushe, su daina cin zarafi domin su yi wa kasa hidima ta hanyar da aka tsara ga rayuwarsu.

Buhari a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya Boade Akinola ya fitar a ranar Juma’a a lokacin kaddamar da titin Sokoto-Tambuwal-Kontagora-Makera mai tsawon kilomita 304km.

Shugaban

wanda ya samu wakilcin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen cika alkawarin da ta dauka na baiwa ‘yan Najeriya hanyoyin sadarwa masu inganci da da nagarta.

An ambato shugaban kasar yana lissafta irin cin zarafi da suka hada da Oba lodi ga ababen hawa da manyan motoci da zubar da man fetur da kuma mayar da kafadun titin zuwa wuraren ajiye motoci na dindindin.

Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa Sanata Adamu Aliero, ya ce tun da aka gina hanyar a shekarar 1973 ba a yi wani gagarumin gyara ba har ya zama tarkon mutuwar Al’umma

Mai martaba Sarkin Yauri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi, ya ce gyaran hanyar na da matukar muhimmanci ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma da kuma makwabtan kasashen ECOWAS.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *