Shugaba Buhari Yana Jagorantar Babban Taron Kasa A Fadarsa Dake Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Jagorantar Taron yau alhamis, ya jagoranci zaman taron majalisar tare da tsohon shugaban kasa Jonathan ya halarci Fadar Shugaban kasa, Abuja kan Taron.

An yi Irin wannan taron ƙna karshe a watan Janairun wannan Shekarar, sai yau kuma da aka karayi.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun halarci taron.

Sauran wadanda suka halartar taron sun hada da Shugaban Ma’aikata ga Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Bello da Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

Tsohon

shugaban mulkin soja Ibrahim Babangida, tsohon Shugaban kasa Abdusalami Abubakar da Ernest Shonekan da kuma Gwamnonin Jihohi suna halartar taron ta hanyar taron bidiyo a Yanar gozo daga jihohinsu.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *