Shugaba Buhari zai gina tashoshin wutar lantarki na kimanin Naira Bilyan 11.3bn a yankin Masarautar bichi Garin surukansa dake Jihar Kano.

Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu ne ya mika kokon baran ga Gwamna Abdullahi Ganduje Kan ya taimakawa Gwamnatin Tarayya da Fili domin gina kananan tashsohin masu taransfoma biyu kowannensu mai karfin 60MVA a Garin Bichi da kuma kauyen garin Kanye.

Wasikar da ministan ya aike wa Gwamna Ganduje ta ce tuni Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya isa garin Bichi da Kanye domin fara aikin gina tashoshin da za su ci Naira biliyan 11.3 —kowannensu Wanda zai lashe Naira biliyan 5.6 — amma rashin fili ya hana a fara aikin.

Idan

aka kammala aikin, tashoshin biyu za su rika samar da wutar lantarkin ne ga yankin Arewacin Jihar Kano Wanda ke karkashin masarautar Bichi

Saboda haka Ya Mai Girma Gwamna, za mu yi farin ciki idan ka amince ka ba wa TCN izini da filayen da za a yi wadannan ayyukan a Karamar Hukumar Bichi da garin Kanye,” inji wasikar ministan.
A watan Maris ne dai tsohon Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Sale Mamman, ya sanar cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince a gina kananan tashoshin wutar lantarkin Bichi da Kanye dake Jihar Kano da Zaki Biam a Jihar Binuwai da sauransu.

An bayar da ayyukan wutar lantarkin na Kano ne bisa bukatar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin.
A Lokacin da majiyarmu ta nemi jin ta bakin Gwamna Ganduje game da lamarin, ya bayyana cewa shi gwamnatinsa ta kosa ta ga an fara aikin kuma za ta ba da filaye da duk abin da ake bukata daga gare domin a gina sabbin tashoshin wutar lantarki.

Idan baku manta ba a Ranar 20 ga watan ogusta na wannan Shekara ne ‘dan Shugaban Kasa Yusuf Muhammadu Buhari ya auri gimbiyar masarautar ta bichi wato Zahra Nasiru Ado bayero Wanda Manyan Nageriya suka halarci wajen da aka Daura auren a masarautar ta bichi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *