Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Nageriya da suyi koyi da ‘dabi’un Annabi Muhammadu SAW.

Mai magana da yawun Shugaban kasar na musamman Kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya Bayyana wannan a wata sanarwa da yafutar domin taya Al’umma musilmai Murnar Zagayowar Ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW sanarwar tana Cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya taya al’ummar Musulmi, ‘yan Najeriya mabiya addinai daban-daban da mabiya addinin Musulunci a duk fadin duniya murnar Mauludi-Un-Nabiyy, maulidin Manzon Allah Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

A cikin sakon taya murnar yau ranar Talata, 19 ga watan Oktoba, ranar hutu a duk fadin tarayyar kasar nan, Shugaba Buhari ya ce, “Ina farin cikin mika gaisuwar zaman lafiya, hadin kai da fatan alheri ga al’ummar Musulmi,‘ yan kasa da sauran Musulmai a duk fadin duniya. yayin da suke yin shagulgula da murnar Eid-Maulud. ”

Shugaban

ya bukaci Musulmai da su yi kokari don “yafiya da kusanci da kyakkyawar rayuwa da koyarwar Manzon Allah (SAW) wanda ake murnar bikin ranar haihuwarsa a wannan rana mai albarka. A wannan lokaci mai albarka, ina yi muku fatan alherin yau.”

Shugaban yana amfani da wannan damar don jinjina ga ƙarin ayyukan da Sojoji, Rundunar ‘Yan Sanda, da hukumomin leƙen asiri suka fara don shawo kan ƙalubalen tsaro a cikin ƙasar.

Ya ce gwamnati na sa rai kuma tana da niyyar ci gaba da wannan kokari kuma tana kira ga kafafen yada labarai don magance Matsalar da bayar da rahoto kan matakan tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *