Shugaban Jam’iyar APCn riko na Kasa Gwamna Mai mala buni ya goyi bayan Shugabancin Danzago Tsagin Shekarau a jihar Kano.

Rikicin Jam’iyar APC a jihar kano tsakanin tsagin Shekarau da tsagin Ganduje Bayanai na Cewa Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress a Kano Alhaji Abdulmajeed Danbilki Kwamanda ya ce kwamitin rikon jam’iyyar APC na kasa karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni na goyon bayan bangaren Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Kano.

Danbilki Kwamanda ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan rediyon Vision FM da ke Kano.

Abdulmajeed

Danbilki Kwamanda ya ce lokacin da Mai Mala Buni da Sanata Ahmad Lawan suka zo Kano a ranar 1 ga watan Janairu 2022 domin halartar daurin aure da jaje, shugaban riko na kasa yayin da yake gaisawa da Sanata Barau Jibril da Malam Shekarau ya bukaci su cire mayafin da suka rufe.

A kan cire mayafin nasu shugaban riko na kasa Mai Mala Buni ya shaidawa Sanata Barau da Malam Shekarau cewa muna goyon bayan ku, in ji Danbilki Kwamanda.

Tun a ranar 16 ga watan Oktoba shugabannin jam’iyyar APC a Kano ke fama da rikici tsakanin Ahmadu Haruna Zago da Malam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Abbas na bangaren Gwamna Ganduje ke marawa baya.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da taron jam’iyyar da bangaren G7 ya gudanar a ranar 16 ga watan Oktoba wanda ya samar da Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Kano.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *