Sojojin Nageriya sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP mutun Hamisin 50 a Karamar hukumar askira Uba ta jihar Borno.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kawar da ‘yan ta’addar ISWAP a wani samame na baya-bayan nan da suka kai a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, birgediya-janar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, a Abuja

Mista Nwachukwu ya ce farmakin da suka kai ya kai ga kashe manyan kwamandojin ISWAP da ‘yan sanda da yawa.

Ya ce sojojin sun kuma ragargaza wata motar ‘yan ta’adda ta Mine-Resistant Ambush Protected (MRAP) da kuma manyan motoci da bindigu da dama.

Mista

Nwachukwu ya ce sojojin na 115 Task Force Battalion a ranar Asabar sun yi artabu da ‘yan ta’addar ISWAP a Askira Uba.

“Sojojin sun kuma kwato manya-manyan makamai da alburusai da suka hada da, Motoci Biyar Bindiga, Bindigogin Kare Jiragen Sama guda biyu, Bindigogin AK 47 guda biyar, Bindigan HK guda daya da kuma bindigogin HK guda daya.

“Haka zalika, sojojin na 115 Task Force Battalion sun gudanar da wani samame na asuba zuwa kauyen Leho da kewaye, inda suka gano gawarwakin ‘yan ta’addan guda uku da suka tsere, sannan kuma sun kwato harsashi 2,560 na 7.62mm Special da harsashi 29 na 7.62mm na NATO da ‘yan ta’addan suka yi watsi da su.

“A wani samame na daban, sojojin sun kuma samu nasarar kwato bindiga kirar AK 47 guda daya tare da gano wata na’ura mai fashewa a wani sintiri a kauyen Karawa da yankin Dam Fish Dam. Duk a jihar borno

“Tawagar sashin kawar da ababen fashewa sun lalata bama:baman da ‘yan ta’addan duka shirya in ji shi.

Mista Nwachukwu ya ce babban hafsan sojin kasa (COAS), Faruk Yahaya, Laftanar-Janar, a ranar Lahadin da ta gabata ya jagoranci tawagar manyan hafsoshin sojin Najeriya domin kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Kwamanda 28 Task Force Brigade, Dzarma. Zirkusu, da kuma jajantawa iyalan jaruman da suka rasu. A fagen daga.

(NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *