SOYAYYA DA SOJA: Wani Matashi Ɗan bautar ƙasa ya Nemi Soyayyar Wata Sojar da Take Basu Horo, Kuma Ta BaSa amsar Data Dace.

Hausawa sunce garin masoyi baya nisa. Duk inda mutum yake, sai yaje ya ɗauki abinda Allah ya ƙaddara rabon sane abin nan.

Wani Faifan bidiyo, ya nuna wani matashi na nuna ƙauna da neman auren wata soja , wacce suka haɗu a wani sansanin bada horo na ƴan bautar ƙasa dake can Jihar kwara.

An dai daura Faifan bidiyon ne a kafar sadarwa ta Instagram, inda acikin bidiyon idanuwa suka ga matashin dan bautar ƙasar, ya tsuguna da gwuiwoyin sa a ƙasa, sannan ya zaro zoben soyayya , su kuma sauran ƴan uwansa ƴan bautar ƙasa ba abinda suke sai ihu gamida jinjina gare sa.

class="wp-block-image size-full">

Koda ya zaro zobensa keda wuya, tuni saurayin ya kamo hannun sojar batare da jin tsoro ba, ya saka mata zoben a hannun ta, gamida janyo ta jikinsa, wanda kai daka gani kasan tana cikin matuƙar farin ciki.

Rahotanni da dama dai since lamarin ya faru ne a sansanin horar da masu bautar ƙasa dake jihar Kwara.

Domin kallon Faifan bidiyon, latsa nan

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *