Suleiman Hashim wanda yayi tattaki daga lagos zuwa Abuja domin Murnar cin zaben Buhari ya shiga harkokin Fina finan hausa.

Sulaiman Hashim wanda aka fi sani da Trekker, wanda shine yayi tattaki da Jihar Lagos dake kudu maso yammacin Nageriya zuwa babban birnin tarayya Abuja don murnar lashe kujerar Shugaban ƙasa da Shugaba Muhammed Buhari yayi a zaben 2015 zangon farko, Suleiman daga Karshe dai yanzu ya zama Jarumin masanaantar Shirya fina finan Hausa ta Kannywood.

Sulaiman Trekker, ya fara da fitowa ne a cikin shirin masanaantar Kannywood mai dogon zango Labarina na kamfanin saira Movies wanda ake haskawa a tashar Arewa24.

Idan

kuka kula da kyau shine likitan daya tafi da ‘dan wasa Mai suna Presidor zuwa ƙasar waje don duba lafiyar kwakwalwar sa a cikin shirin.

A wata tattaunawa da ‘dan Jarida Shuaibu Abdullahi, Sulaiman ya ce ba bacewa yayi ba dama kafin Shugaban ƙasa Muhammedu ya ci zabe ai yana harkokin sa kuma bayan an ci zabe ma ya koma harkokin sa kamar yadda ya saba, dama yayi tattaki ne saboda soyayya ga Buhari da kuma alƙawari da rantsuwa da yayi a kan hakan.

Duk da dai ko wace Gwamnati ana samin kura kurai amma ban taba dana sanin yin tattaki saboda nasarar Buhari ba kuma har yanzu ɗan gani kashenin Buhari ne ido kulle; inji shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *