SUNA LINZAMI: Ana Zargin Hafsat Idris Barauniya da lamushe kuɗin wani kamfani har Naira miliyan daya da dubu ɗari uku (N1,300,000).

Wani shahararren kamfanin shirya finafinan Hausa dake garin Kano mai suna UK entertainment ya lafta shahararriyar yar fim ɗin Kannywood ɗin nan mai suna Hafsat Idris wacce akafi sani da suna Barauniya a gaban wata kotu dake Ungogo ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Abdullah.

Kamfanin, yana zargin jarumar ne abisa zargin cewa sun lale kuɗi sun bata kimanin Naira Miliyan ɗaya da dubu dari uku da zummar zatayi musu wani shiri mai taken “Girke-Girken

Africa”.

Zargin kuma ya ƙara da cewa, Hafsat Idris harma ta soma yin shirye shiryen, amma kuma tun kafin aci talata da laraba a shirin, sai ta tsere.

Wanda hakan ne yasa sukayi ƙarar ta, suna neman taimakon Shari’a, akan ta taimaka ta dawo musu da wancan kuɗi, sannan kuma ta biya su diyyar Miliyan goma abisa sasu tafka asara da sukayi, watau tserewar datayi tasa an samu tsaiko a harkar.

To sai da Hafsat Idris Barauniya bata halarci zaman kotun ba, hakan ne yasa aka daga karar zuwa ranar sha tara ga wannan watan da muke ciki, watau Oktoba 19, 2021 domin ci gaba da wannan shari’ar.

Sannan kotun tayi umarni, da asake sada ta da sammaci.
Allah ya kaimu ranar.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *