Ta tabbata Bola Ahmad Tinubu zai tsaya takarar Shugaban kasar Nageriya.

A jiya daya ga watan daya 2022 Hon Abdulmumin Jibrin Kofa a matsayin sa na babban daraktan kungiyoyi magoya bayan Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakoncin gidajen jaridu kimanin dari a gidan sa na garin kofa, Bebeji Kano. Yayi hira akan siyasan kasa da kuma takarar Bola Ahmed Tinubu. Inda ya bada tabbaci cewa Bola Ahmed Tinubu zai yi takarar kujerar shugaban kasa 2023.

Sannan anyi gagarumin taron addua Allah SWT Ya zaunar da kasar mu Najeriya lafiya tare da neman nasara ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023 mai zuwa wanda Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya shirya kuma malamai daga fadin jihar Kano 2,500 ne suka gabatar. Sannan Kofa yayi empowerment na matasa 2,500 wanda aka koyawa sana’o’i daban daban da kuma scholarship ga mata 2,500 wadanda aka zabo daga sassan jihar Kano baki daya. Kowannan su an basu tallafin kudi daga N100,000 zuwa kasa. Taron ya samu halartar manya manya malamai daga dariku daban daban, da manyan yan siyasa, tare da matasa.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *