Tabbas kwankwaso ya ziyarci EFCC amma ba’a Kama shi ba domin ya dawo gida ~Hotoro.

Fitaccen marubuci a gidan Siyasar Kwankwaso, Salisu Yahaya Hotoro, ya ƙaryata batun da aka rawaito a juya, cewa EFCC ta kama tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan zargin sa da wawure kudaden yan Fansho.

Salisu Hotoro ya rubuta a shafin sa kamar haka,  Eh haka ne, Jagoran mu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci ofishin hukumar EFCC a yammacin jiya domin bayar da bayanai tare da kare kansa akan wani ƙorafi da wasu mutane suka kai gaban hukumar ta EFCC suna masu zargin sa da tafiyar da kuɗaɗen hukumar Fansho ta hanyoyin da basu dace ba.

Hotoro

yace Cikin ikon Allah kuma Kwankwaso ya dawo gida tun a daren na jiya bayan ya gama bayar da bayanan nasa, me kuma kuke so ku sani?

A cewar Salisu Hotoro shi dai Kwankwaso ba zargin sa ake da sace kudi ba kuma ba kwashe kudin yai yasa a Aljihu ba.

Hotoro yace Kuɗin Fansho dai ba mayar da su Daloli yayi ya dinga sunƙuma su a aljihu ba, da su ya gina manyan birane na Kwankwasiyya, Amana da kuma Bandirawo Mega Cities, kuma dukkannin waƴannan gine-gine da yayi suna nan har yanzu a matsayin mallakin ƴan Fansho ba mallakawa kansa su yayi ba.

Kuma nayi imani da Kwankwaso ya sauka daga gwamna bai ɗebi waƴancan kuɗaɗen da yawansu ya kai biliyan 10 yayi wancan gidaje ba da tuni babu su babu labarin su a yanzu.

Koma dai menene lokaci zai yi alƙalanci, kuma ai kowa yasa ciki da gaskiya wuƙa bata huda shi.

Jam’iyyar APC ce kuma ba zamu koma ba duk wata barazana da za’ayi mana. Inji Salisu Yahaya Hotoro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *