Tallafin karatu kyauta Gwamna zullum zai biya naira Milyan N476.6m ga dalibai sama mutun dubu sha biyar 15,374 a Jihar Borno.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya fitar da kudi naira miliyan 476.640 domin biyan tallafin karatu na shekarar 2020/2021 ga dalibai 15,374 na jihar Borno a Wasu manyan makarantu. Kwamishinan ilimi mai zurfi da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, Engr Babagana Mallumbe Mustapha ne ya sanar da sakin kudin jiya a Maiduguri, bayan wata ganawa da kungiyar daliban jihar Borno (NUBOSS) a hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno.

Kwamishinan ya ce za a yi amfani da kudin e-e-e don biyan kudaden ga duk wadanda suka amfana.

Babban

sakataren hukumar bayar da tallafin karatu, Malam Bala Isa, ya yi kira ga daliban da za su amfana da su fuskanci karatunsu da gaske. A madadin daliban, shugaban kungiyar dalibai ta kasa reshen jihar Borno (NUBOSS) Sugun Abba, ya yabawa gwamna Zulum bisa yadda yake kishin walwalar dalibai da kuma jajircewa wajen inganta ilimi a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *