Tankar Mai ta Kife a Titin Naibawa Kake Kan Titin Zariya zuwa Kano.

Wata babbar mota ɗauke da man fetur a unguwar Naibawa ta kife a kan akan titi.

Motar mai ɗauke da fetur, kamar yadda rahotanni suka bayyana, cewar ta samu matsala ne, inda nan take ta kama da wuta, sannan ta auwa wani rami dake gefen hanya.

Tuni dai jama’ar dake kasuwanci a yankin da motar ta fadi, suka ranta ana kare tare da cika wandunan su da iska, a wani ƙoƙarin tsira da rai da lafiya da sukayi.

class="has-text-align-justify">Daga karshe, mazauna yankin sunyi kiran gaggawa ga mahukunta da jami’an tsaro domin isa wajen, a samu a shawo kan gobarar.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *