Tinubu zai tsaya takarar Shugaban kasa a 2023 yazo gidana domin neman goyon bayana ~Cewar Tanko Yakasai.

Babban jigo a Kungiyar kungiyar Arewa Consultative Forum kuma dattijo a jihar Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana cewa zai goyi bayan takarar shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.

A ranar Laraba ne Tinubu ya ziyarci dattijon a gidansa da ke Abuja.

Yakasai ya shaidawa majiyarmu bta PUNCH a ranar Asabar cewa tsohon gwamnan Legas ya je gidansa da ke Abuja domin neman goyon bayan sa ga kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa (Tinubu) a zabe mai zuwa.

A

baya-bayan nan, an ga fastoci da allunan talla da ake yayatawa na takarar shugaban kasa na Tinubu, wanda ya kasance gwamnan Legas daga watan Mayu 1999 zuwa Mayu 2007 a manyan biranen kasar da suka hada da Legas da Abuja.

Duk da dai har yanzu Tinubu bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kowane mukami a shekarar 2023 ba, an samu rahotanni da kuma alamu da ke nuna cewa yana da sha’awar kujerar ta Shugaban Kasar Nageriya.

A watan Oktoba ne Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya kaddamar da ajandar Kudu-maso-Yamma a shekarar 2023, wata kungiyar siyasa da ke neman goyon bayan Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Tinubu, wanda ya yi bikin cikarsa shekaru 69 a watan Maris na 20.

Da yake magana da Asabar PUNCH a ranar Juma’a, Yakasai mai shekaru 96 ya ce ya ware wasu ‘yan siyasa biyu don mara masu baya Zuwa ga matakin Shugaban kasa a 2023.

Sai dai ya ce ba shi da niyyar shiga siyasa amma yana da damar da tsarin mulki ya ba shi na marawa duk wani dan takarar da yake so.

Da aka tambaye shi ko yana shirin shiga jam’iyya mai mulki bayan ziyarar Tinubu, Yakassai ya ce, “Bana son shiga wata jam’iyya (siyasa) amma zan iya goyon bayan dan takarar da na ke so. A 1951 na sha fada cewa ba zan zama dan jam’iyya ba amma zan goyi bayan dan takarar da na ke so.”

A kan ziyarar shugaban jam’iyyar APC, dattijon ya ce, “Shi (Tinubu) ya zo ya kawo min ziyara ne amma a gaskiya ina da mutun biyu daga cikin su (masu takarar shugaban kasa) da na kebe tun farko kuma na sha alwashin cewa kowane daya daga cikinsu. wanda ya fara zuwa neman tallafi na shine wanda zan tallafa. Tinubu ne mutum na farko.”

Da aka tambaye shi ko Tinubu ya ce masa zai tsaya takarar Shugaban kasa a 2021, Yakasai ya ce Tinubu na Sha’awar Haka kuma shiyasa yazo ya nemi goyon bayana.”

Yakasai, ya ce bai bayyanawa Tinubu ba, a lokacin ziyarar, cewa zai goyi bayan burinsa.

Ya kuma ce dole ne masu sha’awar tsayawa takara su fara daidaita matsalolin zaben fidda gwani a jam’iyyunsu daban-daban “sannan za mu fara kwatanta su.”

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *