TIRƘASHI: Gwamnatin Tarayya ta sanar da neman ƙwararrun likitoci guda 74 domin kaisu ƙasar Guinea Bissau.

A yayin da gida bata ƙoshi ba, sai gashi Gwamnatin tarayya ta sanar da neman likitoci guda 74 domin zuwa ƙasar Guinea Bissau yin aiki.

Likitocin Najeriya dai sun kasance suna yawan fita ƙasashen waje domin neman yanayi mai kyau na aiki da albashi zuwa ƙasashe da suka haɗa da Burtaniya, nahiyar turai da Amurka.


Ko kwanaki , sai da ƙasar Saudiya tazo har Abuja tana tantance likitoci da zata jibga takai ƙasar ta, wanda mutane da yawa ke ganin hakan ba komai bane face raini da ita ƙasar ta Saudiya ta nuna ga ƙasa Najeriya.

class="wp-block-image size-full is-resized">


Duk da daga baya, sunce jami’an tsaro sun tarwatsa taron, amma hakan abune da yakamata a fara tsorata, domin yana nuna yadda yanayin lafiya ya zama na innalillahi Wainna Ilaihi rajiun.

Ba kasafai aka cika ganin likitoci daga Najeriya suna tafiya ƙasashen Afirka ba, amma a wannan karon sai gashi Najeriya a matsayin ta yaya babba ita da kanta take neman likitocin domin kaisu wajen.

Jami’an lafiya nada matuƙar muhimmanci kamar jami’an tsaro, amma sai gashi za’a ɗauke su akaiwa wata ƙasa duk da gida bai hana ƙoshi ba.

Dole ne gwamnati tayi duba akan irin wannan abubuwa, musamman guduwar da kwararru sukeyi a daga kasar nan, domin kawo mana sauyi a fannin da hakan ke faruwa ba wai ita kanta ta dinga neman masu ƙarawa miyar gishiri ba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *