TIRKASHI: Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Wani matashin dan achaba ya sha yabo tare da samun tukuici mai tsoka bayan ya mayar da wasu makuden kudi da ya tsinta a titi.

Emmanuel Tuloe ya ji sanarwa inda ake cigiyar makuden kudin a gidan rediyo kuma ya kira tare da mayarwa da masu shi.

A sakamakon wannan nagarta da gaskiya da ya nuna, an ba shi tukuicin kudi har $1,500 wanda ya yi daidai da N616,350.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *