TIRKASHI: ‘Yan sandan Jigawa sun kama wani matashi yana lalata da akuya a Gwaram

Kakakin rundunar ‘yan sanda Jigawa Lawan Shiisu ya bayyana wa ‘yan jarida cewa ‘yan sanda masu patrol cikin dare a Unguwar Kunnadi suka kama matashin mai shekaru 25.

” Yan sanda sun kama wannan matashi mai shekaru 25 ne a daidai yana aikata wannan abu. Ya kama wannan akuya ne da karfin tsiya sannan ya rika saka mazakutar sa a bayan wannan akuya har yan sandan suka kama shi turmi da tabarya.

Shiisu

ya ce an fara gudanar da bincike a kai kuma da zarar an kammala binciken za a kai shi gabar kuliya.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *