TSADAR ABINCI: Majalisar Tarayya ta kafa kwamitin da zai binciki dalilan tsadar abinci da kayan masarufi

Majalisar Tarayya ta kafa kwamitin da zai karaɗe ƙasar nan domin gano dalilan hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi.

Kwamitin wanda aka kafa a ranar Laraba, zai kasance a ƙarƙashin shugabancin Honorabul Peter Akpatason, wanda shi ne kuma Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye.

An naɗa kwamitin bayan Ibrahim Isiaka, ɗan APC daga jihar Ogun ya miƙa tsaye ya yi ƙorafi dangane da yadda rayuwa ta yi matuƙar tsada a Najeriya.

Ya nuna damuwa ganin yadda a cikin shekara ɗaya farashin kayan abinci da na wasu nau’o’in kayan masarufi sun kusa nunkawa a wasu sassan ƙasar nan.

Isiaka

ya ɗora laifin a kan gurguntattun tsare-tsaren kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bijirowa da su.

Sai kuma kamar yadda ya ce, akwai dalilai na kulle kan iyakoki da gwamnatin tarayya ta yi da kuma ƙuncin rayuwar da ya samo asali sakamakon gurgunta tattalin arzikin Najeriya da cutar korona ta yi.

Wannan kwamiti dai zai gana da masu masana’antu, ƙungiyoyin ‘yan kasuwa, manya da ƙananan masu harkokin kasuwanci, Ƙungiyar Masana’antu ta Ƙasa da sauran masu ruwa da tsari a wannan lamari.

An ɗora wa kwamitin nauyin bincikawa da gano dalilan hauhawar farashin da kuma hanyoyin da farashin ke hauhawa, sai kuma hanyoyin shawo kan lamarin.

“Wannan Kwamitin Dukan Kura Da Gwado Ne Kawai” -Honorabul Igbakpa:

An riƙa yin ja-in-ja kafin a kafa kwamitin. Cikin waɗanda aka yi jayayyar da su, har da Ben Igbakpa, wanda ya ce kafa kwamitin ba shi da wani amfani, domin a ƙasar nan kowa ya san dalilan tsadar abinci.

Kan haka ne ya ce kowa ya san wasu tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya ke bijirowa da su ne ke haddasa masifar tsadar rayuwa a ƙasar nan.

Yayin da gwamnatin APC ke ganin cewa ta taka rawar gani, a gefe ɗaya kuma kusan komai sai tsula tsada ya ke yi a ƙasar nan.

Maimakon a ce ana samun sauƙin farashin kayan abinci, duk wanda ya tashi sama, ba ya sake dawowa ƙasa. Idan ka ga ya motsa daga inda ya ke, to sama zai ƙara yi.

Naira na ƙara taɓarɓarewa a kasuwar canji, kusan gidajen masu ƙaramin ƙarfi a garuruwa duk an daina girki da ita ce, sai gawayi. Yayin da gas kuma ya yi tsada.

Albashi bai ƙaru ba, riba sai raguwa ta ke yi, amma kuma a kullum kayan abinci sai tashi sama farashin su ke yi.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *