TSARO: Yan Nageriya Karku sa rai da samun wani sabon Al’amari daga Buhari da Gwamnatin sa ~Cewar Obasonjo

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce sa ran shugaban kasa Muhamadu Buhari zai yi fiye da abin da ya yi, tamkar dukan mataccen doki ne.

Ya yi wannan jawabi ne a Abuja ranar Litinin a wajen wani taro kan tsaro na bai daya da gidauniyar zaman lafiya ta Global Peace da Vision Africa suka shirya.

Obasanjo ya ce: “Gaskiyar magana ita ce: Shugaba Buhari ya yi iyakar kokarinsa. Abin da zai iya yi ke nan. Idan muna tsammanin wani abu fiye da abin da ya yi ko abin da yake yi, wannan yana nufin muna bulala mataccen doki Wanda kuma ba’a bukatar Hakan.

Obasanjo

ya kuma ce matakin soji kadai ba zai kawo karshen tada kayar baya a kasar nan yadda ya kamata ba.

Ya ce kamata ya yi a yi amfani da tsarin Kai tsaye na ha’din kai wajen tunkarar kalubalen tsaro.

“Mutane suna magana game da ra’ayin siyasa, amma ina magana akan aikin siyasa ne Nufin siyasa bai wadatar ba. Dole ne a yi daidai da aikin siyasa. Inji Obasonjo.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *