Tuna baya: a Kashe duk wanda aka kama da laifin karɓar rashawa da cin hanci Kamar yadda china take yi ~Cewar Ganduje

A wani tsohon bidiyon dake yawo a kafafen sada zumuntar Zamani an hango Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Yana magana da harshen turanci Yana Mai Cewa ya Kamata duk wanda aka Kama da laifin Cin Hanci da Rashawa, kawai a kashe shi Kamar yadda Kasar China Sukeyi Ganduje ya fa’di Hakane a Lokacin da yake Gabatar da Wata Makala A Taron Gyaran tsarin Siyasar Nigeria a Shekarar, 2005.

Idan baku manta ba dai Gwamna Ganduje shine wanda bidiyon sa na karɓar dalolin Amurka ya bulla a Shekarar 2018 wanda Jaridar Daily Nigerian  ta wallafa mallakar Ja’afar Ja’afar.

Kawo

yanzu dai Jama’a na cigaba da CeCe kuce Kan bullar bidiyon ganin Cewa haryanzu Gwamnatin Shugaba Buhari Bata dauki wani mataki ba dukda kokarin Gwamnatin a fannin yaki da Rashawa.

Ga. Bidiyon a Sha Kallo. Lafiya.

https://www.jaridarmikiya.com/wp-content/uploads/2021/11/Video-61.mp4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *