Wallahi ‘Yan uwa ku kiyayi kanku da aibata wasu mutane a wuraren Maulidi da cewe basu Annabi Muhammadu SAW ~Cewar Sheikh Ibrahim Makari


A wani sakonsa da Futyanu media ta wallafa Shehun malamin ya na Mai cewaa wai basa son ANNABI (Sallallahu Alaihi Wasallam), wannan kuskure ne babba, domin kalmar shahada ta hadamu da duk wanda ya amsa suna “Musulmi”
.
Don haka su din ma kuskure ne da rashin fahimta yasa ba suyin maulidin, tayiwu duk ranar da suka gane cewa ashe fa maulidin nan alkhairi ne babba, to kai da kake gadara ko tutiya kanayi idan ba kayi da gaske ba sai sunzo sun fika hidima da samun muradi acikin maulidin.
.
Mu

bama fada da kowa, kuma bama gaba da kowa, kuma bama qin kowa sai dai idan mutum yazo mana da wani abu ko halayya wanda ya saba da Shari’a da kuma Manhajin da muke kai
.
Hakan ma fa ba wai mutumin zamu qi ba, A’a halin nasa ko abin da yakeyi zamu Qi
.
Domin shi din bawan Allah ne kuma dole muyiwa bawa duban Maigidansa.
.
Allah ya karawa Malam Lafiya da Nisan Kwana Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *