Wani attajiri ɗan Najeriya, ya gwangwaje wata yarinya da rabin miliyan, saboda halayyar kirki data nuna.

Attajirin

Mutumin dai, an hango sa yana rubutawa matar cek na dubu ɗari biyar ne a gafen hanya.

Hakan kuwa ya biyo bayan fantsama mata da ruwa da ɗaya daga cikin jerin gwanon motocin sa suka yi wa matashiyar yayin da take wucewa ta gefen hanya..

Yawanci idan irin wannan abin ya faru, mutane sunayin yawanci na maida martani ne da zafafan kalamai, inda wasu har zagi sukeyi.

To amma a wannan gwadaben, matashiyar batayi komai ba, hasali ma, share jikin ta tayi a tsanake, sannan taci gaba da tafiyar ta.

Wannan

abin data yi, ya janyo hankalin mutumin mai suna Marksman Chinedu Ijiomah.

Ai kuwa nan take, ya sauko daga kan motar da, ya ƙarasa wajen datake, yayi mata magana, sannan ya bata haƙuri, a madadin ma’aikatan sa.

Bayan ya bata haƙuri ne sai zance ya ɓarke, inda yake tambayar ta, ko me takeyi a rayuwar ta domin rayuwa.

Budurwar sai tagaya masa cewar, tana aikin ɗinki ne.

Ai kuwa ashe kakarta ce ta yanke saka, nan da nan yayi tunani gamida bata zunzurutun kuɗi har rabin miliyan ɗaya, watau Naira dubu ɗari biyar, domin ta bunƙasa sana’ar ta.

A wani hoto daya wallafa a shafin sa na Facebook, mutumin yace:

“Nan da nan, na umarci motoci suyi parking sannan na kira budurwar don neman afuwa a madadin tawaga ta. Tabbas, lokacin da ta zo, mun ba ta haƙuri kamar yadda kalmomi za su iya isarwa kuma na tambaye ta abin da ta yi don rayuwa kuma lokacin da ta ce ita mai zanen kaya ce, mun yi tunanin mafi kyawun hanyar da za mu taimaka mata kuma daga ƙarshe muka sanya hannu kan bata tallafin rabin Naira miliyan ɗaya watau (500k).”

Ya kamata dukkanmu mu ƙi gudanar da duk wani ayyukan da ke sanya wasu cikin wurare marasa daɗi kuma kada mu taɓa ƙarfafa shi.

Amma kwanciyar hankali da wannan baiwar ta nuna yana da zurfi sosai kuma bai kamata a yi watsi da shi ba.

Allah yasa ayyukanmu ta fuskar yanayin rashin kwanciyar hankali ya sa wasu su sake tunani.

Allah yasa ta koyar da wasu muhimman darussa game da rayuwa.

Link:
BBC report:
Man’s Profile:

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *