Wani Jami’in tsaro ya kwashe Gwamna da mari a daidai Lokacin da yake tsaka da jawabi a kasar Iran.

A Wani taron gabatar da sabon gwamnan Iran ya katse a ranar Asabar bayan da wani mutum ya taka kan dandamali ya mari shi a fuska.

Zeinolabedin Khorram, sabon gwamnan lardin gabashin Azarbaijan, na ian wani mataki na gabatar da jawabi a masallacin Imam Khumaini da ke birnin Tabriz a arewa maso gabashin kasar a lokacin da lamarin ya faru.

Wani faifan bidiyo da kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya wallafa ta yanar gizo, ya nuna wani mutum cikin nutsuwa yana tafiya zuwa Khorram, inda yana Zuwa ya wanke shi da mari a fuska sannan kuma ya yi masa bulala. Ana iya ganin jami’an tsaro a guje wajen wanda ya aikata laifin suna jan shi daga kusa da Gwamnan.

Wani

abu ne da ba kasafai ake samun tashe-tashen hankula ba a Iran — taron ya samu halartar ministan harkokin cikin gida na kasar, da wakilan ofishin Ayatullah Khamenei da sauran jami’an gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tasnim cewa, wanda ya aikata laifin a mai suna Ayoub Alizadeh, wani jami’in rundunar sojin kasar ne.

A wata hira da gidan talbijin na IRIB, gwamnan lardin ya ce shi da kansa bai san mai laifinsa ba.
Haryanzu Ba a dai san dalilin kai harin ba. A cewar Khorram, wanda ya aikata laifin ya shaida wa ‘yan sanda bayan kama shi cewa ya mari shi ne saboda ya ji haushin yadda wani mutum namiji ya yi wa matarsa ​​allurar rigakafin cutar ta Covid-19, maimakon mace, in ji IRIB a cikin rahotonta.

Wani rahoto ya ce harin ba na siyasa ba ne. Da aka tambaye shi game da abin da ya faru a majalisar dokokin kasar a ranar Asabar, Ali Alizadeh, wakilin birnin Maragheh da ke lardin Gabashin Azarbaijan, ya ce, “tabbas, dalilin wannan mutum na kashin kansa da kansa ne, kuma ba shi da alaka da nadin Gwamnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *