WATA SABUWA: Gogarman ‘yan bindiga Turji ya fice daga dajin Zurmi, ya kafa hedikwata a yankin Isa a Sokoto, yana ‘kokarin sake shiri

Matashin gogarman ‘yan bindiga Turji, ya yi gaba da rundunar sa daga dajin Zurmi cikin Jihar Zamfara zuwa yankin Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto.

Muhammad Bello, wanda aka fi sani da Turji, ya bar dajin Fakai cikin Karamar Hukumar Zurmi tun kafin sojoji su fara ragargazar dajin da ya yi sansani shi da yaran sa.

Sau da dama ya na yin fatali da ƙoƙarin yin sulhu da Gwamnatin Jihar Zamfara.

Sau ɗaya ne ya ce a shirye ya ke a yi sulhu da shi, wato a lokacin da Sheikh Ahmed Gumi ya kai masa ziyara a sansanin sa, a Zurmi cikin Jihar Zamfara.

Kusan

tsawon watanni biyu kenan Turji ya na riƙe da mahaifin Kakakin Majalisar Jihar Zamfara, kawun kakakin da kishiyar mahaifiyar kakakin, waɗanda ya tura yaran sa su ka kamo masa su a ƙauyen Magarya, mahaifar Kakakin Majalisar Zamfara, Nasiru Magarya.

Mun buga yadda wani kwamandan Turji mai suna Ɗan Bukkolo ya shaida wa masu kai kuɗin fansa cewa Turji ya ce su koma da kuɗin su, ya fasa sakin mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara ɗin da sauran dangin sa da ya ke riƙe.

Hijirar Turji Daga Zamfara Zuwa Isa A Sokoto:

Majiyoyi daga sassa daban-daban, har da cikin jami’an tsaro sun shaida cewa Turji ya kafa hedikwata tsakanin dajin Tozai da Suruddubu cikin Ƙaramar Hukumar Isa, a Jihar Sokoto.

“Turji ya kafa hedikwata kilomita huɗu bayan an wuce ƙauyen Tozai kafin a kai ƙauyen Suruddubu.” Inji wata majiya.

Shugaban Ƙungiyar Rundunar Adalci ta Jihar Sokoto, Bashir Altine, ya ce ya yi amanna cewa Turji ya gudo ne daga Fakai zuwa Tozai da Suruddubu domin ya kauce wa ruwan hare-haren da sojoji ke kaiwa.”

Altine ya ce matakan da Jihar Zamfara ke ɗauka a yanzu ya na shafar su sosai.

Ya ƙara da cewa al’ummar Tozai da Suruddubu da kewayen su babu abin da za su iya yi.

“Yanzu zai iya kai hare-haren a Isa da Isa ta Arewa kan sa tsaye babu mai iya tare masa hanya.” Inji Altine.

Majiya a cikin jami’an tsaron Katsina sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga da dama na ta canja wurin kafa sabbin sansanonin su.

Akwai Wata Tsiyar Da Turji Ke Ƙullawa:

Wata majiya daga Sabon Birni, da ke zaune a Sokoto, ta shaida cewa ba mamaki akwai wata tsiyar da Turji ke ƙullawa ko shiryawa, shi sa ya kafa hedikwata tsakanin Tozai da Suruddubu a Jihar Sokoto.

“Idan ka lura, Turji ya shirya da gogarman ‘yan bindigar yankin Shinkafi da Sabon Birni, Halilu Sububu. Kai ko babu taimakon Halilu da yaran sa, Turji zai iya kai wa kowane ƙauye hari.”

Majiya ta ce yaran Turji da na Halilu ne su ka kai wa sojoji mummunan hari a yankin Dama.

“Turji ne da kan sa ya jagoranci kai harin. Saboda ya sha aika wa mazauna yankin wasiƙar cewa ya gano su na kai wa jami’an sojoji rahoto kan Turji ɗin. Kuma ya sha aika saƙo ga sojoji da sauran jami’an tsaro, ya na gaya masu cewa zai kai hari, kuma harin da zai kai, zai yi muni sosai.”

Dama Sanata Ibrahim Gobir ya shaida wa Zauren Majalisar Dattawa cewa ‘yan bindiga sun tare a yankin mazaɓar sa, saboda a can babu yawan sojoji masu kai masu hare-hare.

Daga. Ahamd Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *