WATA SABUWA: Na shirya siyar da kaina – In ji wani matashi da talauci ya ishe shi a Kano

Wani matashi mai suna Aliyu Idris, ya bayyana cewa a shirye yake ya siyar da kansa saboda tsanin talauci.

Aliyu ya bayyana cewa a lokacin da ya shigo garin Kano daga Kaduna, ya nemi aikin dako a kasuwar kwari amma aka ana shi saboda babu wanda ya san shi kuma ba a yarda da shi ba.

Ya kuma sha alwashin yin biyayya ga duk wanda ya siye shi matukar bai sabawa addinin Musulunci ba.

Daga

Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *