Wayyo…Ina son kamanni na nada su dawo — Inji ɗan daudu Bobrisky mai siffar mata, bayan anyi masa tiyatar sauya halitta an samu akasi.

Bobrisky

Idrisu Okuneye, wanda ya fi shahara da Bobrisky, ya yi koka sosai akan illar aikin kwalliyar canja halitta da aka yi masa kwanan nan, hakan ya biyo bayan samun matsalar da aikin yasamu ne.

Bobrisky

Matashin mai shekaru 28 ya yi iƙirarin cewa za a yi masa aikin ne don taimaka masa samun ƙarin jikin mata.

To amma sai dai, Bobrisky yanzu ya ce:

Yana son rayuwarsa ta dawo yadda take da, saboda yanzu haka idan ya kwanta, da wuri ɗaya kawai yake iya barci, kuma hakan ya faru ne na tsawon tsawon kwanaki.

A cewarsa:

“Ciwon yayi tsanani gaskiya…domin ji nake kamar zan mutu”.

Bobrisky wanda ya rubuta hakan a Snapchat, ya ƙara da cewa:

“Na yi nadama da na kasance a wannan yanayi na kwanan nan !!! Hakika Ina cikin ciwo mai radadi… Wannan aikin na lipo 360 yana mun zafi sosai (rage naman bayan mutum domin ya fitowa mutum zanen dirin ƙugu da siffa). Ina son jin dadina ya dawo. Cikina yana mun zafi, da bayana sosai.

“Mafi muni acikin zafin duka shine bacci a wuri ɗaya duk rana… Wayyo”.

Bobrisky dai ya kasance mutum mai son ado, da ƙwarewa irinta mata, kuma ya daɗe da barin Najeriya, domin zuwa Najeriya.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *