Ya kamata gwamnati Masu hannu da shuni da talakawa suyi tanadi, duba da yadda hatsi ya samu gagarumin lalacewa saboda ruwan daya yanke. Martanin masu bibiyar Mikiya.

Sanin kowa me cewar, daminar bana kakarta tazo da wani yanayi na ha-ila-ha-ula-i, sakamakon damina datazo a makare kuma ta tafi da wuri a mafi akasarin yankunan arewacin kasar nan.

Saboda haka ne, shinkafa da dawa, gero da maiwa ya samu gagarumin yankewa yayin da yake tsaka da haɗa yabanya.

Akwai wani bawan Allah daya je gona, ya tarar shinkafar sa bazata yanku ba, nan take yasa ashana ya cinnawa gonar wuta gabaki dayanta.

class="has-text-align-justify">Wasu manoman kuma, da yawa, sukan samu shinkafar, amma ba yadda sukayi zaton zasu samu ba.

Gwamnati yanzu ta hana shigowa da shinkafa, sannan wacce akayi a gida ta samu matsala.

Tabbas, wannan ba ƙaramin ƙalubale bane ga ƙoƙarin da gwamanti take na kokarin ganin, Najeriya ta iya ciyar da kanta a matsayin ƙasa.

Ya kamata, duk wani mai fada aji, yasan cewa, duk yadda aka samu matsala a harkar noma, talauci na ƙara ta’azzara, yunwa na ƙara ƙaimi, doka da oda tana ƙwacewa, sannan duk mai jin yunwa zai iya komai domin ya ƙoshi.

Da Gwamnati, Masu Kuɗi, Talakawa, Ƙungiyoyi, Bankuna, Malamai dole ne su haɗu ko kuma kowa yayi abinda zai iya domin ganin farashin abinci bai ƙara tashin gwauron zabi ba. (Dama ƙaƙa bare hakan ta faru).


Zasu yi hakan ne ta hanyar:

Gwamnati: Gwamnati ta samar da wai tsari da zai mayar wa da manoma asarar da suka yi, ko kuma ta biya su adadin abinda suka saba girba a kowacce shekara na daga hatsi. Ta samar musu da tallafi na taki domin kaka mai zuwa, iri mai kyau tare da gina musu rijiyoyin burtsatse domin warware irin wannan matsalolin a nan gaba.

Masu Kuɗi: Su bada bashi maras kuɗin ruwa, sannan su tallafawa waɗanda wannan iftilain na fari ya shafa tun kafin abin ya ta’azzara.

Talakawa: Suyi tanadi na abinci tun yanzu, domin yanayin yana nuna, da alama abinci zai iya tashin gwauron zabi, indai ba wani ikon Allah ba.

Ƙungiyoyi: Su wayar da kan mutane akan akan amfanin noma da iri mai saurin nuna ba irin wanda aka saba amfani dashi tunzamanin iyaye da kakanni ba. Sannan su haɗa gwamnati da manoma na asali, ba manoman ofis ba, manoman da iftilain nan ya shafa domin jin kukansu na kai tsaye.

Bankuna: Su bawa manoma tallafi tunda.

Malamai: Malamai na islamiyya suyi ta addu’a ga Allah s.w.a domin ya kawo mana sauki, tare da jan hankali ga gwamnatin kan taimaka wa manoma da abinda ya shafa.

Allah ya kyauta , ya kawo mana sauƙi.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *