“Ya Sayyadi” da “Ya Sayyada” sunsha ɗaurin talala saboda bawa hammata iska a gaban ɗalibai, hartakai ga Sarawilin “Ya sayyadi” ya kwaɓe, nan fa ɗalibai suka ɓarke da dariya.

Wasu gungun ɗalibai sun kwashi kallo a islamiyya, yayin da aka samu Saɓani tsakanin malamin su da wata malama a islamiyya.

Tunda fari dai, tun a shekarar 2019 aka gurfanar da A’isha Aliyu da A’isha Salisu da kuma Bello Muhammad a gaban kotun majistire mai lamba 35 ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Huda Haruna, inda ake tuhumar su da zargin tada hankalin jama’a.

Jami’in kula da gudanar shari’ar kotun, Ibrahim Maccido ya karantowa waɗanda ake tuhuma laifin su, inda dukansu basu musa ba, suka amsa laifin su.

class="wp-block-image size-full">

A lokacin rikici ne ya ɓarke tsakanin su, inda suke koyar da yara a makarantar, hakan yasa suka fito har kan titin unguwar dake Darmanawa suna ta faɗa da hayaniya, to ana cikin haka ne aka yiwa ya Sayyadi aika-aika, aka kwaɓe masa Sarawili, ɗalibai kuwa suka ce me zasuyi inba suita darawa ba.

Bayan haka ne, sai kotu ta gargade su gamida basu umarnin su zauna lafiya, a lokacin hakan bai yiwu ba, inda suka ƙara afkawa cikin rigimar, awannan lokacin ake zargin an fasawa ɗaya daga cikin matan kai.

A halin yanzu dai kotu ta sake yi musu ɗaurin talala, an kuma ɗage zaman kotun har zuwa ashirin ga watan sha biyu na wannan shekarar, domin ci gaba da Shari’a.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *