Yadda wuta ta ragargaji wani babban shashen jami’ar Bayero dake Kano.

Daya daga cikin dakin

A jiya juma’a ne dai wani babban iftila’i ya afkawa jami’ar Bayero dake garin Kano.

Hakan ya faru ne sakamakon wata gagarumar wuta data kama sashen karatu na ɓangaren “Biochemistry” na jami’ar.

Kayayyakin bincike na maɗuɗan miliyoyin nairori ne suka samu lalacewa, wanda maida su, sai anyi babban yunkuri. Duba da muhimmanci da sashen yake dashi ga ɓangaren rayuwar al’umma.

class="wp-block-image size-full">

Domin dakine na bincike. Kawo iyanzu dai, ba’a gama harhaɗa bayanan tarin dukiyar da aka rasa, amma anyi tabbacin cewa, an rasa kuɗi mara misaltuwa, gine gine, tare da muhimman abubuwa.

Daya daga cikin dakin

Bugu da ƙari, ba’a bada sanarwar rasa rayuka ba, ballantana ummul-aba’isin faruwar gobarar ba.

Haƙiƙa a wannan yanayi da ake ciki, ya kamata gwamnati da masu hannu dashi su kaso wa jami’ar tallafi domin gyara wannan waje mai muhimmanci.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *