‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon gwamna Yari, sun yi garkuwa da kanin matarsa

‘Yan bindiga sun kai farmaki Talata Marafa, mahaifar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, sannan suka yi awon gaba da wani surukinsa.

Maharan sun kai hari garin ne a yammacin ranar Litinin, inda suka yi garkuwa da surukin tsohon gwamnan da kuma matar makwabcinsa.

Rahoton ya nuna cewa wannan shinro ne karo na farko da ake kai hari hedkwatar karamar hukumar Talata Marafa. Karamar hukumar ta fuskanci hare-hare a baya, kamar su garkuwa da dalibai sama da 300 a makarantar sakandaren mata ta gwamnati, Jangebe, amma duk a kauyuka suka faru.

Wani

hadimin Yari, Bello Ruwan Bado, ya tabbatar da sace Auwal Hussain wanda aka fi sani da Sarki.

Hussain, wanda ya kasance kanin uwargidar Yari, yana zaune ne a gidan tsohon gwamnan kafin yayi aure kuma an ce yana daya daga cikin makusantan Yari.

Hakazalika maharani sun kuma yi garkuwa da matar makwabcin Hussain, Surajo. Wani makwabcinsa mai suna Mustapha Lawan, ya ce ya ji karar harbi da muryoyin ‘yan bindigar.

Ya ce: “Mun ji lokacin da ‘yan bindigar suka zo da daddare. Sun zo ne a kan Babura sannan suna ta harbi a sama domin tsorata mutane. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare.

“Tun da har ‘yan bindigar za su iya shigowa yankin nan da ake ganin ya fi kowanne tsaro a Talata Marafa, wacce ta kuma kasance gari na biyu a mafi girma a jihar, toh lallai abun tsoro ne. sun shafe sama da awa daya ba tare da jami’an tsaro sun zo don kalubalantarsu ba.”

Ya ce: “Kwanan nan Sarki ya dawo daga Dubai, kuma a lokacin da ‘yan bindigar suka zo, sun ma tambaye shi ko ya kawo wani abu daga Dubai. Kuma basu yi garkuwa da kowa ba baya ga matar makwabcin sarki.”

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *