‘Yan Bindiga sun kashe mutun sittin 60 sun kone kauyaku biyar 5 a jihar zamfara.

Rahotanni daga Jihar zamfara na Cewa Akalla mutane 60 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a kauyukan jihar Zamfara.

Wasu daga cikin kauyaku da abin ya shafa sun hada da Kurfa Danya, Kurfa Magaji Rafin Gero, Tungar Isa da Barayar Zaki a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka a jihar.

Wani mazaunin unguwar mai suna Babangida ya bayyana cewa: “Sun zo da adadi mai yawa kuma a kan babura suna harbin jama’a tare da kona gidaje da shagunan abinci. Mazauna yankin, musamman mata da yara, sun yi tururuwa zuwa wurin tsira.

“Wasu

daga cikinsu suna fakewa ne a karamar hukumar Bukkuyum Har yanzu ba a san inda wasu daruruwan mazauna wurin suke ba. Har ya zuwa wayewar garin ranar alhamis, ‘yan gudun hijira na ci gaba da yin tururuwa a unguwar Nassarawa Burkullu. Wasu daga cikinsu sun samu munanan raunuka sakamakon harbin bindiga.”

Mazauna yankin sun ci gaba da cewa gawarwakin wadanda aka kashen ana ci gaba da diba domin binne su. Sun ce mutane da yawa na fargabar shiga cikin daji mai zurfi don kwaso gawarwakin mutanen da aka kashe.

“Shugaban ‘yan bindigar da aka fi sani da Shehu Bayade shi ne ke jagorantar kai hare-hare da garkuwa da mutane da kuma satar shanu a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi na jihar.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *