‘Yan Bindiga Sun kashe ‘yan Sanda mutun bakwai 7 a jihar zamfara.

Rahotanni daga jihar zamfara na Cewa Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda mutun bakwai a wani harin kwanton bauna da suka yi a hanyar Tofa zuwa Magami a karamar hukumar Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Majiyar rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa an kona daya daga cikin ‘yan sandan da ba a iya gane su ba, inda aka ce an cusa gawarsu a cikin buhu.

An ce hudu daga cikinsu suna dauke da mukamin sufeto a Gidan ‘yan sanda. An bayyana sunayensu kamar Markus Donal, Solomon Amfemi, lshaya Stephen da Gambo Nura. Sai wani Sajan Abdul Garba da wasu biyu.

Wata

majiya da ke zaune a unguwar da lamarin ya faru ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin a lokacin da jami’an ‘yan sanda ke yankin suna sintiri.

‘Yan bindigar, a cewar majiyar, sun banka wa motar ‘yan sandan wuta bayan sun kashe su.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun yi artabu da jami’an ‘yan sandan kafin su kashe su

Ya bayyana cewa an kwashe gawarwakin jami’an zuwa Gusau babban birnin jihar ta zamfara.

Kakakin asibitin kwararru na Yarima Bakura Gusau, Awwal Ruwan-doruwa ya tabbatar da cewa an kawo gawarwakin ‘yan sandan da aka kashe bakwai asibitin.

Anyi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Mohammed Shehu ya ci tura bai Kuma tura Sako ba ya zuwa Yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *