‘Yan Bindiga Sun sace Sabuwar Yar bautar Kasa A kan Hanyarta ta Zuwa Sansanin Yan bautar kasa NYSC a zamfara.

Rahotanni Dake Zuwa Mana nacewa Wasu ‘yan bindiga da ake zargin’ yan fashi ne sun yi garkuwa da wata yar bautar kasa mai suna lorlima Jennifer Awashima

A cewar masu majiyarmu ta Bakin direban motarsu da ya kubuta yace dalibar jami’ar jihar Benue tana kan hanyar ta ne na zuwa sansanin NYSC da ke jihar Kebbi domin gabatar da hidimar ta da Kasa Nageriya a Rukunin Batch C Stream One na 2021, lokacin da aka sace ta tare da wasu fasinjojin motar tare.

Lamarin

ya faru ne a jiya ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba a daidai kewayen jihar Zamfara. Direban motar da wasu wasu an ce sun yi nasarar tserewa daga ‘yan fashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *