‘Yan Bindiga sun tare Hanya sun kashe mutun shida 6 a jihar zamfara.

An kashe mutane 6 tare da yin garkuwa da wasu da dama a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wa masu ababen hawa a hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi a jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, ‘yan bindigar sun kona wasu motocin da aka kama tare da mutanen da ke cikin su, kuma an kasa gano gawarwakin fasinjojin da aka kashe.

Sun ce ‘yan ta’addan wadanda galibinsu Turji ke jagoranta sun tsananta kai hare-hare a yankin Shinkafi – Kaura Namoda bayan farmakin da sojojin saman Najeriya suka kai inda suka kashe kanwar sa da mijinta da kuma wasu sojojin kafa na sa.

“’Yan

ta’addan sun tare hanyar ne a wani wuri tsakanin Kwanar Jangeru da Moriki, kuma tun daga lokacin da matafiya suka daina zirga-zirgar hanyar saboda rashin tsaro. Babu wanda zai iya zuwa dauko gawarwakin fasinjojin da aka kashe a wannan titin,” in ji wani mazaunin garin, wanda ya gwammace a sakaya sunansa.

“Kun san harin da NAF ta kai ta sama a baya-bayan nan ya jawo fushin su. Ya afkawa wasu sansanoni na Turji bayan an fitar da da yawa daga cikin iyalansa da yaransa,” inji wani mazaunin garin mai suna Mansur.

Sai dai wasu mazauna garin sun ce ‘yan ta’addar dauke da makamai sun zafafa kai hare-hare kan jama’a domin nuna rashin amincewarsu da rufe kasuwar dabbobi da aka dade a garin Shinkafi.

An ji wasu daga cikinsu na cewa za su ci gaba da kai hare-hare kan al’umma tare da sace masu ababen hawa har sai an bude kasuwar dabbobi.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce, “Ba ni wani lokaci; Zan dawo gare ku.”

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *