Labarai

‘Yan Jam’iyyar PDP 12 Sun Mutu A Hadarin Mota A Hanyar Zamfara.

Spread the love

Lamarin ya farune akan titin Tsafe zuwa Gusau da yammacin jiya, Laraba da misalin karfe 6 na yamma.

Motoci 4 ne suka hade a hadarin. Kakakin jam’iyyar PDP a jihar, Alhaji Faruku Shattima ya tabbatarwa Punch haka. Yace mutanen suna kan hanyar tarbar gwamnan jihar, Bello Matawalle ne da ya dawo daga Abuja bayan ziyarar aikin da ya kai.

Yace sun yi taho mu gama da wata motar Dangote inda nan take su duka suka mutu.
Mun fahimci an yi jana’izar marigayan da misalin karfe 10 na safiyar yau, Alhamis, Kamar yanda Addinin Musulunci ya tanada.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button