‘Yan Sandan sun kashe ‘Yan ta’adda masu tarin yawa a jihar katsina.

Rundunar Yan sandan Nageriya sun samu nasarar kashe‘ yan fashi 15, sun kamo mutun 50, sun ceto mutum 20, sun kwato shanu 220 a a jihar ta katsina Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta cafke akalla‘ yan fashi 50 tare da ceto shanu 220 a cikin jihar. Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Sanusi Buba-Sanusi, ya ce an kama mutanen ne tare da kwato su a yayin zangon na biyu na yakin da take yi da‘ yan fashin da makami masu satar shanu da kuma satar mutane a jihar. A cewarsa, sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigogin AK 47 guda 9, bindigogin gida 20, motoci biyu, da kuma babura 20.

Ya

ce, “A cikin wannan lokacin da ake dubawa, rundunar ta gudanar da samame daban-daban a wurare da dama a cikin kananan hukumomin da me fama da rikincin, sun fatattaki tare da cafke wasu da ake zargin ‘yan ta’addan ne da ke addabar jihar ta Katsina. Game da yaki da fyade, kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa wannan runduna ta kame masu fyade 140 ya kara da cewa dukkansu an gurfanar da su a gaban kotu don fuskantar hukunci…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *