‘Yan Social Media Sune Matsalar Nageriya ~Cewar Nuhu Ribadu.

Jigo a jam’iyyar All Progressives Congress, Nuhu Ribadu, ya dora alhakin mafi yawan kalubalen kasar a kan labaran karya da kafofin sada zumunta ke yadawa. Ne

Ribadu ya ce “kafafen sada zumunta a yau, wani bangare ne ke da alhakin abin da ke faruwa a kasarmu ta hanyar kokarin inganta abubuwan da ba gaskiya ba da kuma haifar da rarrabuwar addini da kabilanci da Sauran su in ji Mista Ribadu ya Fadi hakane a wani taron manema labarai ranar Lahadi a Abuja.

Mista

Ribadu ya kira taron be domin karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana zargin wasu manyan jami’an gwamnati da daukar nauyin ‘yan fashi a kasar. Ya lura ne bayan da ya Fara karbar tambayoyi daga abokai da sauran hulda da ke neman Jin Gaskiyar Batun.

Tsohon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya ce ya “sha wahala sosai” Sakamakon rahoton da bashi san komai akai ba.

Ya yi kira ga gwamnati da kamfanonin kafofin sada zumunta da su yi amfani da hanyoyin da za su hana yada labaran karya.

“Ba sa yi mana adalci, kuma ina tsammanin gwamnati tana da wani aiki da alhakin daukar mataki, domin babu wanda zai aminta daa yin hakan,” in ji Mista Ribadu. “Kamfanonin kafofin watsa labarun su ma suna da rawar da za su taka, ban ga wani dalili da ya sa Facebook, Twitter, da Instagram za su ba da damar irin wannan lalatacciyar sanarwa ta Cigaba da fita ba tare da sun takarar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *