‘Yan uwan ​​buhari na daura da katsina baki ‘daya sun yaba da biyayyar Gwamna Yahaya Bello ga Shugaba Buhari suna rokonsa da ya tsaya takarar Shugaban Kasa a 2023.

Wata tawaga a Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina, ta yabawa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello bisa goyon bayan da yake bai wa shugaban kasar ba tare da turjiya ba.

Kungiyar masu ruwa da tsaki ga al’adu da siyasa daga Daura sun kai wa Gwamna Bello ziyarar ban girma a jiya ranar Alhamis.

Da yake jawabi ta bakin mai magana da yawun su Injiniya Mato Daura, tawagar ta bayyana cewa, soyayyar Gwamna Bello ga Shugaban kasa ta kasance Wacce ba a taba ganin irinta ba, kuma ta hanyar alakarsa ta kut-da-kut, wasu halaye da dabi’u sun Kara ingata cigaba kala-kala

Mato

ya kuma bukaci Gwamna Bello da ya nuna ra’ayin sa a zabe mai zuwa na 2023 Kan Batun tsayawa takarar Shugaban cin kasar yana mai tabbatar masa da cewa kungiyar za ta yi na’am da shi a matsayin dan takarar da suka fi so da kauna

A nasa martanin, Gwamna Yahaya Bello ya godewa tawagar bisa irin wannan jin martabashi da aka yi, inda ya kara da cewa butulu ne kadai ba zai yaba ga aikin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *