Yanzu-yanzu: Buhari ya sake jaddada gargadin sa ga ‘yan kungiyar IPOB a cikin martanin da ya mayarwa Tuwita

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa” Dakatar da Twitter na wucin gadi da gwamnatin Najeriya ta yi, ta yi hakan ne badon saboda an goge ruburun shugaba Buhari bane, an yi hakan ne saboda Twitter ta zama kafa mafi yada labaran karya da kuma tada husuma a Najeriya”.

“Duk da haka, cire rubutun shugaba Buhari da Twitter suka yi tamkar sun kunya ta shi ne. Abin da Twitter suka yi katsalandan ne, kasancewar basu san halin da Najeriya take fuskanta ba”.

“Saboda haka shugaba Buhari yana gargadin sauran kafofin yada labarai da su shiga taitayin su”.

“Sannan muna so Twitter su sani cewa ‘yan kungiyar IPOB suna karkashin ikon gwamnatin Najeriya ne, saboda haka baza mu taba lamuncewa da abin da suke aikatawa ba”.

“Don haka ba gudu ba ja da baya gwamnatin Najeriya zata dauki mataki kan su”. Inji Shugaba Buhari

Daga Nasara

One thought on “Yanzu-yanzu: Buhari ya sake jaddada gargadin sa ga ‘yan kungiyar IPOB a cikin martanin da ya mayarwa Tuwita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *