Za’a sayawa ‘yan sandan Nageriya barkonan tsohuwa na Bilyan 5.5bn domin kwantar da tarzoma .

Gwamnatin Tarayya a asusun Rundunar ‘yan sandan Najeriya na shirye-shiryen kashe Naira Bilyan N1.85bn wajen horar da ‘yan sanda dabarun kare hakkin dan adam da kuma kare wuraren da ake aikata Manyan laifuka.

Wannan wani bangare ne na Naira biliyan 10 da aka gabatar a matsayin karin ku’din da za’a kashe ga rundunar ‘yan sandan Najeriya kamar yadda yake kunshe a cikin kasafin kudin 2022 na NPTF da aka gabatar wa majalisar dokokin kasar domin amincewa.

Daga

Naira Biliyan 10, Asusun ya ware Naira miliyan 5,871,595,000 na kayan aikin ‘yan sanda da sauran kayan sawa; N1,535,098,724 don horarwa ta cikin gida; da kuma wata naira N1,850,000,000 domin koyarda “dabarun mayar da martani ga zanga-zangar tayarda kayar baya da kula da wuraren aikata laifuka da kuma ‘yancin ɗan adam.”

Hukumar NPTF za ta kashe Naira 1,039,170,593 wajen sayan mai ga motocin ‘yan sanda guda 350 kan lita 30 ko kuma N153,000 a kowace rana.

Har ila yau NPF Asusunta zai sayi ‘kayan hana tarzoma’ ko kuma hayaki mai sa hawaye na N5.5bn da Kuma makamai da harsasai na N4bn, kayan kariya na ma’aikata (rigunan Sulke) akan N2,511,141,100, da Tsarin Bin Saƙon Makamai na Trackfire WTS akan N2,274,928,846.

Haka kuma NPF Zata samar da motocin aiki na musamman na N5,852,211,368, motocin sintiri na N5,170,800,000, ‘sauran motocin aiki’ da kudinsu ya kai N3,984,000,000, da motocin bas din jin dadin ma’aikata da kudinsu ya kai N1,400,000,000.

Haka kuma hukumar ta NPTF za ta gina Cibiyar Taro na IGP akan kudi Naira Biliyan 1, tare da gina katafaren kayan yaki na zamani da zai ya lakume wani N1bn.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *