Zainab Aliyu kila wacce akayiwa sharri da safarar muggan kwayoyi daga Nageriya Zuwa saudiyya ta Shiga hukumar yaki da muggan kwayoyi NDLEA ta Nageriya.

Zainab Aliyu Kila, wata ‘yar jihar Jigawa da wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta shiryawa sharri a yayin da take tafiya zuwa aikin Hajji a kasar Saudiyya a shekarar 2018, ta shiga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.
Miss Aliyu na cikin sabbin jami’an NDLEA 2,000 da aka horar a makarantar horas da jami’an hukumar da ke Jos, jihar Filato a ranar Juma’a.

Mahaifinta, Habibu Kila, ya tabbatar wa da majiyarmu ta DAILY NIGERIAN shigar ‘yar sa hukumar ta NDLEA a ranar Asabar, inda ya ce an tura ta aikin hukumar a matsayin mataimakiyar jami’ar yaki da muggan kwayoyi.

A

ranar 26 ga Disamba, 2018, Miss Aliyu, wacce a lokacin daliba ce a Jami’ar Maitama Sule, Kano, hukumomin Saudiyya sun kama su bisa zargin tafiya da jakunkuna dauke da haramtattun abubuwa da ake kyautata zaton tramadol ne.
Ta yi tattaki ta filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano International Airport, MAKIA, domin yin aikin Hajji mafi karanci, ita da mahaifiyarta, Maryam, da kanwarta, Hajara.

A filin jirgin sama na Jeddah, Hukumomin Saudiyya sun damke jakar, inda daga bisani suka gano Miss Aliyu tare da kama ta a dakinta na otal.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar Saudiyya ta tuhume ta tare da tsare ta tsawon watanni hudu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Bayan wasu kiraye-kirayen da iyayenta da kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula suka yi, hukumomi sun gano cewa barayin miyagun kwayoyi tare da hadin gwiwar ma’aikatan filin jirgin saman Kano sun sanya wa wata jaka dauke da magungunan da sunan ta.

An sake ta ne bayan hukumomin Najeriya da na Saudiyya sun gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa ba ta da wani laifi.

An saki Miss Aliyu a ranar 30 ga Afrilu, 2019 kuma ta dawo gida bayan makonni biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *