Zamu cigaba da taimakon Nageriya Kan yaki da ta’addanci ~Cewar Amurka.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da tallafawa kokarin Najeriya na yaki da ta’addanci da kuma karfafa cibiyoyin dimokuradiyya.

Wannan na kunshe ne a cikin sakon taya murna da Blinken ya fitar a ranar Juma’a don taya Najeriya murnar cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

A cewar Blinken, kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu ta samo asali ne daga sadaukar da kai ga dimokuradiyya da hadin gwiwar tsarin kasuwanci.

“A madadin gwamnatin Amurka da jama’ar Amurka, ina mika sakon fatan alheri ga jama’ar Najeriya a bikin cikar su shekaru 61 da samun ‘yancin kai,” in ji shi.

“Hadin

gwiwa mai karfi tsakanin kasashenmu biyu ya ta’allaka ne akan jajircewarmu na bai daya ga dimokuradiyya da banbance -banbance da ruhin kasuwanci iri daya.

A matsayinmy na abokan aikinku, za mu ci gaba da tallafawa kokarin Najeriya na yaki da ta’addanci da rashin tsaro, inganta tsarin kiwon lafiya, karfafa cibiyoyin dimokuradiyya, inganta mutunta ‘yancin dan adam, da karfafa ci gaban tattalin arziki ciki har da kasuwanci da saka hannun jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *